Tarihin Dattijan Arewa: Shin ko kunsan waye Iya-Abubakar? Kuma wacce rawa ya taka a harkar ilimi a k

Posted by Patria Henriques on Monday, April 22, 2024

- Farfesa na farko a jami'ar Ahmadu bello a shekaru 28 kacal

- Dan Arewa na farko da ya kwashi digiri aji na farko wato first class a jami'ar Ibadan

- Dan Arewa na farko da ya kwaso digirin digirgir a kasar Ingila a Cambridge

A waiwayen mu na yau kan tarihin manyan kasar nan, zamu duba ko waye Iya Abubakar, wanda ya kafa tarihi a ciki da wajen kasar nan a fannin ilmin boko, dalibi mai hazaka da ya sha kan turawa ya baiwa duniya mamaki. A kananan shekaru ya kai matsayin da a yanzu sai dattijai ke iya kaiwa.

Farfesa Iya Abubakar ne dan Najeriya na farko da ya kai matakin Farfesa a jami'ar Ahmadu Bello a Zaria a shekaran 1963, a fannin kimiyyar lissafi a mafi karancin shekaru na samartaka. Yana dan shekara 28 ya kai wannan matsayi da a yau sai mai furfura ke kaiwa. A bangaren lissafi yayi fice, kuma ya zaga duniya sosai kan iya lissafi da wasa kwakwalwa

Farfesa Iya Abubakar, ya kamalla digirin sa na farko a fanin Lissafi daga jami'ar Najeriya da ke Ibadan, inda ya fita da ajin farko, wato first class, dan arewa da ya bada mamaki a kudancin kasar nan. Har ila yau shine mutum na farko daga arewacin Najeriya da ya fara kamalla digirin digirgir a Jami'ar Cambridge da ke Ingila.

Ya zama shugaban sashen lissafi da kimiyar na'ura mai kwakwalwa (wato computer) a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria yana dan shekaru 32 kacal a duniya.

Farfesa Iya, shine dan kasar Najeriya na biyu da ya jagoranci ragamar shugabancin jami'ar a lokacin ya da shekaru arba'in da haihuwa.

Daga bisani, Farfesa Iya Abubakar yayi marabus daga aikin malanta a lokacin da dan kai shekaru 44 a duniya.

To mai karatu, kwatanta da samarin mu na yanzu, wadanda sai sun kai 40 din ma suke fara niyyar nutsuwa su ce wai yanzu suka yi hankali zasu fara tsimi da tanadi, wannan tahaliki ya zama gwarzo, jarumi, kuma babban dattijo da ya kafa tarihi a harkar ilmin boko a arewacin najeriya, dama duniya baki daya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kGpna29kYsGivsihoKdllJbBtbXJmqVmmaKaxKJ50qGgp2WbpHqswc2smKdlp5bGpnnIsphmmZKqr6K3wKtkpK2dlnq4rcKcnGaqkayubsXAZqtnoKSiuQ%3D%3D